Shugaban APC a Edo ya yi barazanar amfani da AK-47 kan masu adawa da zaɓen Tinubu
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, Jarrett Tenebe, ya fuskanci suka bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta inda yake barazanar amfani da bindigar AK-47 kan duk wanda ya yi ƙoƙarin hana jam’iyyar samun kuri’u miliyan 2.5 ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Tenebe ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi aiki tuƙuru don tabbatar da cewa ta samu kuri’u miliyan 2.5 ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya tsaya a hanyar wannan buri zai fuskanci wutar AK-47.
Wannan furuci ya haifar da martani mai zafi daga jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wadda ta bayyana kalaman a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya da kuma ta’addanci maimakon siyasa. Jam’iyyar ADC ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan wannan magana ta Tenebe.
Har ila yau, ƙungiyoyin farar hula sun nuna damuwarsu kan yadda ake amfani da kalaman barazana a cikin harkokin siyasa, inda suka jaddada cewa kuri’ar zaɓe (PVC) ce makamin da ya kamata a yi amfani da shi wajen zaɓen shugabanni, ba bindiga ba.